Wenger zai saye sabbin 'yan wasan baya

Wenger
Image caption Arsenal tayi fama da matsalar 'yan wasa baya a bana.

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya tabbatar da cewa zai saye sabbin 'yan wasan baya a kaka mai zuwa.

Arsenal dai ta shafe shekaru biyar bata daga kowane kofi ba na gasa.

Wenger yace "Bamu da matsala a gaba amma dai a baya da kyar muka sha".

Ya kara da cewar an shamu kwallaye 40 babu yadda zamu iya lashe gasa, amma dai zan gyara.

Arsenal ta kamalla kakar wasan bana ne a matsayin ta uku akan tebur bayan ta lallasa Fulham daci hudu da nema a wasanta na karshe.