Jonny Evans ya sanya sabon kwantiragi

Jonny Evans

Dan wasan baya na Manchester United Jonny Evans, ya sanya sabon kwantiragi a klub din na tsawon shekaru hudu. Kociyan Manchester Sir Alex Ferguson ne ya tabbatar da haka, lokacin da yake hira da gidan talabijin na Manchester.

Ya ce Evans ya samu kwakkwaran ci gaba tun bayan da ya zo klub din daga Sunderland a kakar wasanni biyu da ta gabata.

Ya kara da cewa mun dade muna tattaunawa kan hakan a 'yan kwanakinnan, kuma ina farin ciki da faruwar hakan.

Evans ya taka leda har sau 64, mafi yawan lokutan idan Rio Ferdinand ya samu rauni.