Kofin gasar kwallon duniya ya isa Afrika ta Kudu

Daya daga cikin filayen da za a taka leda a gasar ta bana
Image caption Daya daga cikin filayen da za a taka leda a gasar ta bana

Dubban 'yan kasar Afrika ta kudu ne suka bi dogon layi har na tsawon awanni a birnin Cape Town domin daukar hoto da kofin gasar kwallon kafa na duniya.

Kofin wanda aka sarrafa da zinare an fara zagayawa da shi fadin kasar ne kafin fara gasar a ranar 11 ga watan Yuni.

Sai dai ka'ida ta nuna cewa babu wanda za a bari ya taba kofin sai shugaban kasa da kuma masu rike da kanbun.

Da isar kofin dai babban jami'i na hukumar FIFA Jerome Valcke, ya dauke shi zuwa ga tsohon shugaban kasar Nelson Mandela.

Mr Valcke yace Mandela na daya daga cikin wadanda suka fitar da tsarin gasar ta bana, domin haka bai kamata azo da kofin Afrika ta Kudu ba tare da an kai masa ba.