Chelsea za ta yi kaka-gida a gasar Premier-In ji Ancelotti

Kociyan Chelsea Carlo Ancelotti
Image caption Kociyan Chelsea Carlo Ancelotti

Kocin Chelsea Carlo Ancelotti ya ce yana son ganin Chelsea ta yi kaka-gida a gasar premier ta Ingila, bayan ya jagoranci kungiyar ta lashe gasar premier a shekarar farko a matsayin koci.

Tun a shekara ta 2006 ne rabon Chelsea ta daga kofin sai a bana bayan ta casa Wigan daci takwas da nema a ranar Lahadi.

Ancelotti yace"ina son in shafe lokaci mai tsawo don daga kofinan gasa da yawa".

Carlo Ancelotti dai ya kulla yarjejeniya ta tsawon shekaru uku ne da kungiyar Chelsea bayan ya bar kungiyar AC Milan.

Ya kara da cewar "muna da 'yan wasa na gani na fada daga nan zuwa wasu shekaru masu zuwa".

Ancelotti dai ya maye gurbin Guus Hiddink ne a matsayin kocin Chelsea a ranar daya ga watan Yulin shekara ta 2009 bayan ya shafe shekaru takwas a matsayin kocin AC Milan inda ya lashe gasar Serie A sau daya sannan kuma ya daga kofin zakarun Turai sau biyu.