Man City na gabda sayen Boateng daga Hamburg

Kocin Manchester City Roberto Mancini ya ce kungiyar na gabda kulla yerjejeniya da dan wasan kasar Jamus Jerome Boateng.

Ana hasashen cewar City za ta biya kungiyar Hamburg pan miliyan goma sha daya don sayen dan wasan mai shekaru ashirin da daya wanda yake taka leda a tsakiya ko a baya.

Mancini yace"Muna gabda sayen dan wasan.Boateng dan wasa ne me kyau gashi matashi kuma yana da karfi".

"Yana bugawa kasar shi kwallo kuma akwai alamun cewar za mu saye shi. Zai iya buga wurare da dama ko a tsakiya ko a baya ko a gefe",in ji Mancini.