West Ham ta sallami Zola daga kungiyar

Gianfranco Zola
Image caption West Ham dai ta sallami Zola ne saboda rashin nasaran da ta samu a kakar wasan bana

Kungiyar West Ham da ke Ingila ta sallami kocinta Gianfranco Zola bayan shekaru biyu a kan aiki.

Kocin mai shekarun haihuwa 43 ya bugawa Chelsea wasa a shekarun baya, kuma ya karbi ragamar aikine daga Alan Curbishley a kungiyar a watan Satumbar shekaran 2008.

A lokacin daya kama aiki a kungiyar, ya sa hanu ne a kwantaragin da zai sa ya yiwa kungiyar aiki na tsawon shekaru hudu.

A kakar wasan farko da Zola ya jagoranci kungiyar, kungiyar ta kare ne a matsayin na tara a gasar sai kuma a gasar bana da ta kare a matsayin na goma sha bakwai.