Barcelona ta lashe gasar La Liga

'Yan Barca
Image caption Barcelona ta lashe gasar La liga sau biyu kenan a jere

Barcelona ta lashe a gasar La liga ta Spaniya a karo na biyu a jere karkashin Kocinta Pep Guardiola.

A ranar karshe na gasar dai Barca din ta casa Real Vallodolid ne daci hudu da nema inda ta samu maki 99 cikin wasanni 38.

Dan wasan Vallodolid Luis Prieto ne ya ci kansu da farko kafin Pedro Rodriguez ya zira kwallo daya sannan kuma Lionel Messi yaci biyu.

Ita kuwa Real Madrid ta tashi kunen doki ne wato daya da daya tsakaninta da Malaga duk da kudade fiye da dala miliyan 200 data kashe wajen siyen Cristiano Ronaldo, Kaka, Karim Benzema da Xabi Alonso a kakar wasan bana.

Har wa yau, a kakar wasan bana dai sau daya tal ne aka doke Barca kuma gwarzon dan kwallon duniya Lionel Messi shi kadai ya zira kwallaye 34.