Ina nan daram a Manchester- Berbatov

Berbatov
Image caption Berbatov na fuskantar suka daga magoya bayan United

Dan wasan Manchester United Dimitar Berbatov ya musanta jita jitar cewa zai bar United din a bana, inda yace "zan cigaba da kasancewa a Old Trafford".

Berbatov dai tunda aka siyeshi pan miliyan 30.75 daga Tottenham a shekara ta 2008 ya kasa nuna kanshi abinda yasa aketa alakantashi da kungiyar Bayern Munich da AC Milan ko kuma ya koma Spurs.

Da yake sanarda ritayarshi daga bugawa Bulgariya leda,Berbatov me shekaru 29 ya ce babu inda za shi.

Ya kara da cewar "na zo inda na ke so".

Berbatov ya zira kwallaye 26 cikin wasanni 65 daya bugawa United a shekaru biyu amma dai yana fuskantar matsin lamba saboda ya kasa zira kwallaye da yawa.