An sauya tsarin buga gasar kofin Afrika

magoya baya
Image caption Wasu magoya bayan kasar Angola a lokacin gasar cin kofin Afrika a 2010

Hukumar dake kula da kwallon Afrika CAF ta tabbatar da cewa za a koma buga gasar cin kofin Afrika a shekarun da suka kare da wuturi.

Sanarwa daga adreshin yanar gizon CAF ta ce daga shekara ta 2013 za a soma bin sabon tsarin.

An yanke shawarar ne a shalkwatar hukumar CAF dake birnin Alkahira a Masar a ranar Asabar.

Sauyin ya nuna cewar za ayi gasa biyu a cikin shekara guda wato a Gabon da Equatorial Guinea a shekara ta 2012 sannan kuma a shekara ta 2013 a Libya.

Wannan hukuncin ya nuna cewar a yanzu baza a dinga buga gasar cin kofin kasashen Afrika a shekara guda da gasar cin kofin duniya ba.

A watan Fabarairu Kocin Algeriya Rabah Saadane ya shaidawa BBC cewar duk kasar data tsallake zuwa gasar cin kofin Afrika a shekara ta 2012 tabbas zata buga ne 2013.