Ancelotti na murnar daga kofina biyu

Drogba
Image caption Gwarzon dan kwallon Afrika Drogba ne ya zira kwallon tsakaninsu da Portsmouth

Kocin Chelsea Carlo Ancelotti ya ce kakar wasa ta bana ta biyasu saboda Chelsea ta lashe gasar premier data FA duk a Ingila, a yayinda ta doke Portsmouth daci daya me ban haushi a filin Wembley a wasan karshe na gasar FA.

Didier Drogba ne ya zira kwallo daya daya baiwa Chelsea nasara sannan kuma Petr Cech ya kabe penaritin da Kevin Prince Boateng ya bugawa Portsmouth.

Ancelotti yace "mudai kakar wasa ta bana sai alansan barka".

Kaptin din Chelsea John Terry a halin yanzu dai ya lashe manyan kofina takwas tare da kungiyar Chelsea kuma ya ce sun ji dadin kakar wasan bana.