An dage dakatarwar da aka yiwa Togo

Tamarin hukumar FIFA

Hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA ta dage dakatarwar da hukumar CAF ta yiwa kasar Togo na hanata halartar gasar cin kofin Afrika da za yi a nan gaba.

Hukumar CAF dai ta dakatar da Togon ne bayan kasar ta fice daga gasar da aka shirya a Angola, saboda harin da aka kai mata, a kasar wanda kuma ya yi sanadiyar mutuwar mutane uku.

Hukumar CAF dai ta zargi gwamnatin Togo ne da tsoma baki a harkar kwallon kafan kasar, bayan ta umarci 'yan wasan kasar da su dawo gida domin makokin wadanda aka kashe a harin.

A watan Afrailun daya gabata ne kyaftin din kasar, Emmanuel Adeboye ya ce ya daina takawa kasar leda, saboda harin da aka kaiwa tawagar kasar a Angola.