Nadal ya doke Federer a gasar Madrid

Rafeal Nadal
Image caption Rafeal Nadal ya lashe kyautar Masters sau bakwai

Rafael Nadal ya doke Roger Federer da maki 6-4 7-6 (7-5) inda kuma ya lashe gasar Madrid Open, a yayinda ake shirin fara gasar French Open a mako mai zuwa.

Wanan shine karo na farko da 'yan wasan biyu suka hadu tun bayan wasan da Federer ya doke Nadal a gasar Madrid na bara.

Nasarar da Rafeal Nadal ya yi, shine na goma sha takwas da ya samu kyautar Masters.

Ba'a doke dan wasan a wasanni goma sha biyar da ya buga a jere a jan kasa.