Boateng ya nemi afuwa daga Ballack

Boateng
Image caption Boateng tsohon dan wasan Jamus ne a matakin 'yan kasada shekaru 21

Dan wasan Ghana na tsakiya Kevin-Prince Boateng ya nemi afuwa daga Kaptin din Jamus Micheal Ballack akan bugun da yayiwa Ballack din har ya jawo dan wasan Jamus din ba zai buga gasar cin kofin duniya ba.

Ballack wanda ke takawa Chelsea ya jimu ne a idon sawunshi na dama bayan da suka yi taho mu gama da dan wasan Portsmouth Boateng.

Boateng wanda watakila zai bugawa Ghana wasa tsakaninta da Jamus a rukunin D na gasar cin kofin duniya ya ce bada gangar ya raunata Ballack ba.

Boateng yace"Kayi hakuri, bada gangar bane kuma nayi nadama".

Wannan neman afuwar yazo ne kwanaki uku bayan aukuwar lamarin a filin wasa na Wembley