Essien na fatar samun sauki

Essien
Image caption Essien ne kashin bayan Ghana

Dan wasan Ghana Micheal Essien ya ce zai murmure kafin gasar cin kofin duniya da za a fara a wata mai zuwa.

Tun a watan Junairun bana ne dai dan wasan Chelsea din ya raunata gwiwarshi abinda yasa bai kara taka leda ba.

Essien dai na cikin 'yan wasan da Ghana ta gayyata kuma watakila zai buga wasan sada zumunci kafin a fara gasar.

Essien ya shaidawa Ghanasoccernet.com cewar "ina aiki tukuru don ganin cewar na warke kuma zan iya tabbatar muku da cewar komai zeyi kyau".