Manchester ba zata sayi 'yan wasa ba

Ferguson
Image caption Kocin Manchester United Sir Alex Ferguson

Manajan Manchester United Sir Alex Ferguson yace watakila ba zai siya karin 'yan wasa ba a kaka mai zuwa.

A halin yanzu dai Ferguson ya sayi dan kasar Mexico Javier Hernandez da kuma Chris Smalling daga Fulham.

Ferguson yace "watakila mu sayi karin dan wasa daya, amma dai abin da kamar wuya a irin wanan lokacin saboda kasuwar bata da tabbas".

Ferguson wanda ya bayyana haka a taron manema labarai a Newyork tare da shugabanshi Gill, ya kara da cewar"irin 'yan wasan da muke dasu a wannan lokacin sunyi dai dai idan akayi la'akari da shekarunsu".