FIFA ta ci tarar Masar

Masar
Image caption 'Yan wasan Masar na murnar zira kwallo

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta haramtawa Masar taka leda a birnin Alkahira a wasanni biyu na neman cancantar buga gasar cin kofin duniya a nan gaba, bayanda 'yan kasarta suka kaiwa tawagar Algeriya hari kafin wasa.

An kuma ci tarar Masar na dalan Amurka dubu 88 sakamakon rikicin daya barke a gidanta lokacin wasan a watan Nuwanban bara.

FIFA a ranar talata ta yanke hukuncin cewar Masar zata buga wasanninta biyu na neman cancantar buga gasar cin kofin duniya a shekara ta 2014 akalla a wajen dake da tazarar kilomita dari daya daga babban birninta.

A ranar laraba ne ake saran hukumar kwallon Masar zata maida martani akan hukuncin.

Kwamitin da'a na FIFA ya ce Masar ta kasa tabbatar da tsaron tawagar 'yan wasan Algeriya kafin wasan share fagen a watan Nuwamban bara.