Barcelona ta siye David Villa

Villa
Image caption Sabon dan wasan Barca David Villa

A ranar Juma'a ne Barcelona zata gabatar da David Villa a matsayin sabon dan wasanta bayan ta biya Valencia pan miliyan 34.2.

Dan wasan dai ya kulla yarjejeniya ta tsawon shekaru hudu da Barcelona kuma ya kasance dan wasa na farko da Barcelona ta siya a wannan lokacin sannan kuma Barca din kan hanyar siyen Cesc Fabregas daga Arsenal.

Villa dai ya kasance dan wasan da yafi kowa zira kwallaye a gasar cin kofin Turai a shekara 2008 kuma a baya dai Chelsea da Manchester United sun nuna bukatar siyen dan wasan.

Zuwan shi Barcelona zai kara yawan jita jita akan makomar Thierry Henry da Zlatan Ibrahimovic .