Hukumar Fifa za ta binciki zargin cin hanci

Ingila na necikin masu neman daukar nauyin gasar a shekara ta 2018
Image caption Ingila na cikin masu neman daukar nauyin gasar a shekara ta 2018

Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya Fifa, za ta binciki kalaman da tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta Ingila Lord Triesman, yayi abisa yunkurin neman karbar bakuncin gasar cin kwallon kafa ta duniya a shekara ta 2018.

An jiyo mista Triesman a wata hira da yayi da wata jarida, yana cewa kasar Spain za ta iya janye bukatar ta idan har Rasha wacce itama tana sahun masu nema, ta taimaka mata wajen sayen alkalan wasa a gasar da za a yi ta bana.

Hukumar ta Fifa ta rubutawa hukumar FA ta Ingila wasika inda take neman da a bata cikakken bayani kan kalaman na mista Triesman.

Sai dai hukumar ta FA ta yi alkawarin ba da hadin kai ga hukumar ta Fifa, wacce ka'idojinta suka haramta musayar kalamai tsakanin kasashen da ke neman daukar nauyin gasar ta cin kofin duniya. Wata sanarwa da Fifa ta fitar ta nuna cewa, babban sakataren ta Jerome Valcke, ya nemi kwamitin da'a na hukumar da ya duba kalaman na Lord Triesman kan takarar daukar nauyin gasar ta shekarar 2018 da 2022.