Laurent Blanc zai zama kocin Faransa

Blanc
Image caption Laurent Blanc ya kasance gwarzo a Faransa

Laurent Blanc zai bar kungiyar Bordeaux a matsayin koci don ya maye gurbin Raymond Domenech a matsayin kocin kasar Faransa bayan an kammala gasar cin kofin duniya.

Dan shekaru 44 da haihuwa wanda kuma a tsohon dan wasan Manchester United ne ya jagoranci kungiyar Bordeaux a shekara ta 2009 har ta lashe gasar klub klub na Faransa da kuma kofin kasar, amma a bana ya karke babu komai.

Hukumar kwallon kasar Faransa ta ce "mun kulla yarjejeniya da Laurent Blanc a matsayin kocin Faransa."

Blanc na cikin jerin 'yan wasan da suka taimakawa Faransa ta lashe gasar cin kofin duniya a shekarar 1998 da kuma gasar kofin kasashen Turai a shekara ta 2000.