FIFA ta kokan akan siyen tikiti a Afrika

valcke
Image caption Sakatare Janar na FIFA Jerome Valcke

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta nuna rashin gamsuwarta akan yadda 'yan Afrika basu sayi tikiti masu yawa ba na shiga filayen kwallo lokacin gasar cin kofin duniya.

Sakatare janar na FIFA Jerome Valcke yace tikiti dubu 40 ne kacal aka siya daga kasashen nahiyar Afrika banda Afrika ta Kudu mai masaukin baki.

A baya dai an soki FIFA akan tsarinta na yadda za a sayi tikitin ta hanyar intanet abinda ba kasafai 'yan Afrika ke amfani dashi ba.

Wannan ne karon farko da za a gudanar da gasar cin kofin duniya a nahiyar ta Afrika.

Valcke yace gannin yadda aka fuskanci cikas a Afrika ta Kudu zasu bullo da wata dabara kafin gasar cin kofin duniya a Brazil a shekara ta 2014.