Kanu zai cigaba da kwallo a Portsmouth

Kungiyar Portsmouth ta Ingila ta baiwa kaptin din Najeriya Nwankwo Kanu damar kulla sabuwar yarjejeniya da ita duk da cewar tana fama da matsalolin kudi.

Portsmouth wacce a yanzu ta koma gasar Championship daga gasar Premier, ana binta miliyoyin daloli, amma dai ta ce tanason ta kafa duga duginta da kyau saboda makomarta yayi kyau.

Bayaga Kanu dai, kungiyar ta baiwa David James damar sabunta yarjejeniyarshi.

Amma dai Aruna Dindane da Hassan Yebda zasu koma tsaffin kungiyoyin da suke takawa leda a baya.