James na san zamowa kocin Portsmouth

David James
Image caption James ya dade yana taka kwallo a gasar Premier ta Ingila

Mai tsaron gidan Portsmouth David James, ya nuna sha'awarsa ta horas da 'yan wasan klub din, a cewar jagoran klub din Andrew Andronikou.

Andronikou ya shaidawa BBC cewa: " David ya bayyana sha'awarsa ta zamowa mai horas da 'yan wasa".

Sai dai acewar Albeit, muna ganin yayi wuri idan muka nada shi a kan wannan mukami yanzu.

A ranar Alhamis ne Avram Grant, yayi murabus daga mukamin sa na horas da 'yan wasan Portsmouth, yayinda shi kuma James, wanda ke da shekaru 39, ya kammala kwantiragin sa. James dai na cikin 'yan wasan da ake saran za su takawa Ingila leda a gasar cin kofin duniya, amma Andronikou na so ya tattauna maganar da shi kafin gasar, koda kuwa ba zai samu mukamin ba.