Faransa ta cire Diarra cikin 'yan wasa

Domench da Diarra
Image caption Kocin Faransa Raymond Domenech da Lassana Diarra

Faransa ta cire dan wasan tsakiya Lassana Diarra cikin jerin 'yan wasan da zasu taka mata leda a gasar cin kofin duniya.

Hukumar kwallon kafa ta Faransa ta bayyana cewar dan wasan na Real Madrid na fama da ciwo a cikinshi, kuma zata bashi hutu sai abinda hali yayi.

Kawo yanzu dai kocin Faransa Raymond Domenech bai bayyana wanda zai maye gurbin Diarra ba.

Cikkaken jerin 'yan wasan:

masu tsaron gida: Hugo Lloris (Olympique Lyon), Steve Mandanda(Olympique Marseille), Cedric Carrasso (Girondins Bordeaux)

Masu buga baya: Bacary Sagna (Arsenal), Patrice Evra (Manchester United), William Gallas (Arsenal), Eric Abidal (Barcelona), Sebastien Squillaci (Sevilla), Marc Planus (Girondins Bordeaux), Gael Clichy(Arsenal), Anthony Reveillere (Olympique Lyon)

Masu buga tsakiya: Alou Diarra(Girondins Bordeaux), Jeremy Toulalan (Olympique Lyon), Florent Malouda (Chelsea), Yoann Gourcuff (Girondins Bordeaux), Abou Diaby (Arsenal), Franck Ribery (Bayern Munich) Masu buga gaba: Thierry Henry (Barcelona), Nicolas Anelka (Chelsea), Andre-Pierre Gignac (Toulouse), Sidney Govou (Olympique Lyon), Djibril Cisse (Panathinaikos), Mathieu Valbuena (Olympique Marseille)