Ferguson ya taimaka min-In ji JS Park

Park
Image caption JS Park ya ce zai kara nuna kanshi a Afrika ta Kudu

Kaptin din Koriya ta Kudu Ji-Sung Park ya bayyana cewar kocin Manchester Sir Alex Ferguson ya taimaka mai wajen kara gogewa a kwallo.

Dan wasan ya ce sakamakon haka zai fuskanci gasar cin kofin kwallo da karfinshi a Afrika ta Kudu.

Park ya ce "yayi ammana dani, kuma ya bani kwarin gwiwa sosai".

A matsayinshi na dan wasan Koriya ta Kudu, Park ya buga wasanni 85 kuma ya zira kwallaye 11, kuma yana cikin 'yan wasan da suka kasance na hudu a gasar cin kofin duniya da akayi a shekara ta 2002.