Mourinho zai bar Inter ya koma Madrid

Inter Milan
Image caption 'Yan Inter Milan na murnar lashe gasar zakarun Turai

Jose Mourinho ya ce da alama zai bar Inter Milan ya koma Real Madrid, bayanda ya taimakawa Inter din ta lashe kofina uku a bana.

Inter Milan ta lashe gasar zakarun Turai bayan ta casa Bayern Munich a ranar Asabar, abinda ke nuna cewar Mourinho ya zama koci na uku a duniya daya lashe kofin tare da kungiyoyi biyu daban daban.

Mourinho yace: "ina bakin cikin ganin cewar tabbas wannan ne wasana na karshe a Inter".

Ya kara da cewar"Idan baka zama kocin Real Madrid ba, to lallai ka bar wani gibi".

Mourinho wanda ya bar Chelsea ya koma Inter Milan a shekara ta 2008, ya lashe gasar serie A sau biyu da Inter din da kuma kofin Italiya, sanan kuma ya ce wata rana zai koma Ingila horadda 'yan kwallo.