Ribery zai cigaba a Bayern har zuwa 2015

Ribery
Image caption Ribery ne kashin bayan Bayern Munich

Dan wasan Bayern Munich Frank Ribery ya kulla yarjeniniya da kungiyar na cigaba da kasancewa da ita har zuwa shekara ta 2015.

Dan kwallon Faransan me shekaru 27, a bara Real Madrid da Manchester United duk sunyi zawarcinshi.

Shugaban kungiyar Bayern Karl-Heinz Rummenigge ya ce "Mun yi murna ganin cewar daya daga cikin shahararrun 'yan kwallon duniya ya amince ya kara kulla yarjejeniya damu".

Ribery ya koma Bayern ne daga kungiyar Marseille akan pan miliyan 17 a shekara ta 2007, kuma anyi kewarshi a wasansu da Inter Milan a ranar Asabar inda Diego Milito ya zira kwallaye biyu abinda kuma ya kawo karshen aniyar Bayern din na lashe gasar zakarun Turai a karo na biyar.