Dangote ya musanta aniyar siyen Arsenal

Dangote
Image caption Mujjallar Forbes ta Amurka ta bayyana Dangote a matsayin wanda yafi arziki a Afrika

Attajirin nan a Nigeria, Aliko Dangote, ya musanta rahotannin da kafafen yada labarai ke wallafawa cewa, yana da aniyar siyan wani kaso na kungiyar kwallon kafar Arsenal ta Ingila.

Aliko Dangote ya fitar da wata sanarwa wadda BBC ta samu, inda yake cewa, shi magoyin bayan klub din Arsenal ne, amma ba shi da wata aniyar sayan hannun jari ko kuma mallakar wani kaso a klub din.

Jaridar Sunday Times ce ta bayyana cewar hamshakin dan kasuwan wato Dangote ya nuna muradin sayen kaso 16 cikin 100 na hannun jarin Arsenal da Nina Bracewell-Smith tasa a kasuwa.

Dama dai Stan Kroenke da Alisher Usmanov wadanda keda kaso mafi tsoka a kungiyar ta Arsenal sun riga sun nuna kwadayin sayen kashi sha shidan.