Malouda ya gargadi Manchester United

Malouda
Image caption Malouda yana cikin 'yan wasa da zasu bugawa Faransa a Afrika ta Kudu

Dan wasan Chelsea Florent Malouda ya gargadi Manchester United cewar Chelsea zata bude sabon karni kuma ta cigaba da haskakawa a badi.

Chelsea karkashin jagorancin Carlo Ancelotti ta lashe gasar premier a bana bayan tafi Manchester United da maki guda, amma kuma a wasanta na karshe ta lallasa Wigan Athletic daci takwas da nema.

Bugu da kari Chelsea din ta lashe gasar cin kofin FA inda ta doke Portsmouth a wasan karshe daci daya da nema, abinda kuma ya nuna cewar ta lashe kofina biyu a karon farko a tarihinta na shekaru 105.

Malouda yace"Ina matukar farin ciki kuma ina saran Chelsea zata bude sabon karni".