Ballack ya ce zai cigaba da kwallo a Chelsea

Ballack
Image caption Micheal Ballack a lokacin da Boateng ya fille shi

Dan wasan Chelsea Micheal Ballack ya bayyana cewar zai kara sanya hannu a sabuwar yarjejeniya da kungiyar saboda tana kulawa dashi.

Dan wasan me shekaru 33 wanda ba zai buga gasar cin kofin duniya ba saboda rauni a idon sawunshi, ya ce tunda ya samu raunin kungiyar ke kula dashi, a don haka zai sakankamata.

Yace "ina ganin zan cigaba da zama a Chelsea kuma kocinmu Carlo Ancelotti ya nuna mani karamci a kakar wasa ta bana".

Ballack wanda dan asalin kasar Jamus ne ya ce zai zauna a Stamford Bridge don a bashi damar nuna kwarewarshi a kwallo.

Ana saran a wannan makon ne zai tattauna da shugaban Chelsea Roman Abramovic akan batun kulla sabuwar yarjejeniyar.