Fabregas ya soma horo a Spaniya

fabregas
Image caption Fabregas yayi kuka lokacin daya samu raunin

Spaniya ta kara samun kwarin gwiwa a shirye shiryenta na tunkarar gasar cin kofin duniya bayan dan wasan Arsenal Cesc Fabregas ya fara horo.

Dan shekaru 23, Fabregas bai taka leda tun a watan Afrilu kuma a 'yan kwanakinan anata alakantashi da kungiyar Barcelona.

Fabregas dai ya turgude ne a wasa tsakanin Arsenal da Barcelona abinda kuma yasa wasu ke fargabar ba zai je Afrika ta kudu ba.

Dan wasan dai ya shiga cikin horo gadan gadan tare da sauran 'yan kwallo Spaniya inda 'yan kallo dubu biyu suka shiga fili don kallonsu.

Shi kuwa dan wasan Liverpool Fernando Torres a ranar litinin ya fara horo shi kadai ba tare da sauran 'yan wasa ba.

Torres dai tun a watan Afrilu ne akayi mashi fida kuma yanzu dai ya soma murmurewa.