Najeriya ta tashi babu a wasanta da Saudiya

Super Eagles
Image caption Super Eagles basu ji dadi ba a hannun Saudi Arabiya

Shirye shiryen Najeriya na fuskantar gasar cin kofin duniya da za ayi a karon farko a nahiyar Afrika ya soma gamuwa da cikas inda ta buga wasan sada zumunci tsakaninta da kasar Saudi Arabiya a ranar talata kuma aka tashi babu ci a wasan.

Wannan ne dai wasan farko da sabon kocin kasar Lars Lagerback ya jagoranci 'yan wasan Super Eagles tun bayan da aka nadashi.

A halin yanzu dai wasan sada zumunci tsakanin Najeriya da Columbia da kuma wanda za ayi tsakanin Najeriya da Koriya ta Arewa sune zasu kara nuna zasu kara zama mizanin ganin karfin Super Eagles.

Masu sharhi dai sun dade suna nuna fargabar cewar yadda Najeriya ke shirye shiryenta na gasar da za ayi a Afrika ta Kudu alama ce watakila ba zata iya taka rawar gani ba.

Najeriya dai na rukuni daya ne da kasashen Argentina da Koriya ta Kudu da kuma Girka a gasar cin kofin duniya.