Mikel Obi zai hade da Super Eagles a ranar Juma'a

Mikel Obi
Image caption John Mikel Obi na daga cikin gogaggun 'yan wasan Super Eagles

Dan kwallon Najeriya John Mikel Obi zai hade da sauran 'yan wasan kasar a ranar Juma'a.

Mikel wanda a kwanannan akayi mashi fida a gwiwarshi, an samu fargabar watakila ba zai taka leda ba a gasar cin kofin duniya.

Dan wasan na Chelsea dai bai taka leda ba a wasan sada zumunci tsakanin Najeriya da Saudi Arabiya, amma dai kakakin Super Eagles Idah Peterside ya ce Mikel zai buga sauran wasannin biyu.

Peterside ya shaidawa kickoffNigeria.com cewar an tura jami'an lafiya na Najeriya don su duba dan wasan a London.

Yace "zai kasance tare da mu daga ranar Juma'a, ranar da likitocinshi za su bashi izini".

Najeriya dai na rukunin b ne tare da kasashen Argentina da Girka da kuma Koriya ta Kudu.