Garau nake banda ciwo-Inji Rooney

Rooney
Image caption Rooney ya shahara wajen cin kwallaye

Dan wasan Ingila Wayne Rooney ya musanta rahotannin dake cewar yana fama da rauni yayinda gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya ke karatowa.

Dan wasan me shekaru 24, ya yi fama da ciwo a idon sawunshi a kakar wasan data wuce kuma a wasan da Ingila da doke Mexico a ranar litinin ya samu matsala a wuyarshi.

Rooney yace "Garau nake, bani da wata matsala. Kuma ina cikin horo tare da sauran 'yan wasan Ingila tun lokacin da aka hadamu".

Ya kara da cewar "banda wata matsala a idon sawu na, wannan duk maganar banza ce".

Rooney dai ya kasance daya daga cikin kashin bayan Ingila da take ji dasu a gasar da za ayi a Afrika ta Kudu ganin cewar ya zira kwallaye 34 a wasanshi na Manchester United.