Super Eagles na neman filin karawa da Columbia

Super Eagles
Image caption Najeriya dai na cigaba fuskantar cikas a kokarin buga wasanta da Columbia

Har yanzu Najeriya na neman fili wasan da zata buga wasan sada zumunci tsakanin da Columbia a ranar 30 ga watan Mayu.

Wasan da aka shirya bugawa a filin West Ham wato Upton Park amma sai a ranar litinin West Ham din ta ce ta fasa bada filinta.

Cikin gaggawa sai Najeriya ta maida wasan filin Luton Town Kenilworth Road.

Amma sai a ranar laraba masu filin wato Hatters suka ce Super Eagles su nemi wani filin.

Wata sanarwa da Luton ta fitar ta ce za ayi bukin al'adu a wannan ranar a garin saboda haka 'yan sanda zasu maida hankali ne a wajen bukin al'adun kuma ba zasu iya lura da filin kwallon ba.