Brazil za ta kara da Zimbabwe da Tanzania

Brazil
Image caption 'Yan wasan Samba, sarukanan tamaula

Brazil za ta buga wasannin sada zumunci da Zimbabwe da kuma Tanzania a shirye shiryenta na fuskantar gasar cin kofin duniya.

Brazil za ta fuskanci Zimbabwe ne a ranar 2 ga watan Yuni a birnin Harare ta kuma kara da Tanzania a Dar es Salaam a ranar 7 ga watan Yuni.

Tuni dai bangarorin da abubuwan ya shafa suka amince da kece rainin kafin gasar da za ayi a Afrika ta Kudu.

Kasashen Zimbabwe da Tanzania duk sun ce za su baiwa Brazil kudin amincewa ta kara dasu.