Babu 'yan kallo a wasan Najeriya da Columbia

super eagles
Image caption 'Yan wasan Super Eagles na Najeriya

Magoya bayan Najeriya a Ingila baza su samu damar kallon Super Eagles na taka leda ba kafin gasar cin kofin duniya.

Saboda babu 'yan kallo da zasu shiga fili don kallon wasan sada zumuncin da Najeriya za ta kara da Columbia a ranar Lahadi a Milton Keynes.

Haka ya biyo bayan hanasu filin da West Ham United da kuma Luton Town suka yi don ayi wasan gaban 'yan kallo.

Najeriya dai ta fuskanci cikas matuka a shirye shiryenta na gasar cin kofin duniya musaman ma akan batun wasannin sada zumunci.

Bugu da kari dai a wasanshi na farko a matsayin kocin Super Eagles Lars Lagerback ya buga canjaras wato babu a wasa tsakanin Najeriya da Saudi Arabiya a ranar latanan data wuce.