Ma'aikatan Afrika ta Kudu zasu fara yajin aiki

Kofi
Image caption Kasashe 32 zasu fafata ne akan wannan mulmulen zinaren

Kungiyar kwadagon kasar Afrika ta Kudu ta yi barzanar shiga yajin aiki lokacin gasar cin kofin duniya.

Kungiyar dai ta ce tanason gwamnati ta cire karin data yi akan kudin hasken wutan lantarki.

Sakatare Janar na kungiyar kwadagon kasar COSATU, Zwelinzima Vavi ya ce zasu yi wata tattauna ta musamman a ranar 14 ga watan Yuni lokacin da aka riga aka fara gasar cin kofin duniya don yanke shawarar shiga yajin aikin.

A wani labarin na daban dai kungiyar ma'aikatan sufuri na Afrika ta Kudun, ta ce ta amince da karin albashin da akayi mata, kuma za ta janye yajin aikinta na makwanni uku data fara.