A Faransa za a yi gasar Euro ta 2016

Shugaban Hukumar UEFA Michel Platini
Image caption Shugaban Hukumar UEFA Michel Platini

Hukumar kula da wasan kwallon kafa ta Turai,UEFA, ta baiwa kasar Faransa damar daukar nauyi da shirya gasar cin kofin nahiyar Turai a shekara ta 2016.

Faransar ta doke kasashen Turkiyya da Italiya, wadanda suma suka nemi damar daukar nauyin gasar.

An kai ruwa rana tsakanin Faransa da Turkiyya, inda Faransa ta lashe kuri'u bakwan da aka kada, yayinda Turkiyya ta samu shida. Gasar ta shekara ta 2016, itace irinta ta farko da za ta kunshi kasashe 24.

Shugaban hukumar kwallon kafa ta Farnsa Jean-Pierre Escalettes, ya bayyana wannan rana da cewa mai mahimmanci ce ga kasar.

"Tunda aka bamu damar shirya wannan gasa, to babu shakka za mu ba marada kunya".