UEFA ta amince da dokar kashe kudi a kungiyoyi

Michel Plantini
Image caption Shugaban hukumar UEFA, Michel Plantini

Hukumar kwallon kafa ta Turai UEFA ta amince da sabuwar doka wacce ta haramtawa kungiyoyin kwallon kafa kashe kudaden fiyade wadanda suke samu.

UEFA ta ce matakin zai hana kungiyoyi fadawa matsalar bashi kuma duk wacce ta sabawa dokar tabbas za ta dakatar ta ita da ga buga gasar cin kofin zakarun turai ko kuma ta Europa.

Sabuwar doka dai za ta hana masu mallakan kungiyoyin da su sanya kudadensu cikin kungiyar, kamar yadda kungiyar Chelsea da Manchester City ke yi.

Dokar dai za ta fara aiki ne a shekarar dubu biyu da goma sha hudu.