Obama ya gana da 'yan wasan Amurka

Shugaba Obama
Image caption Shugaba Obama na gaisawa da 'yan kwallon Amurka

Shugaba Barrack Obama ya gana da tawagar 'yan kwallon Amurka a fadar White House, a wani bangare na shirye-shiryen su zuwa gasar cin kofin duniya.

Shugaba yayi amfani da wannan damar wajen yin gargadin cewa 'yan ta'adda za su iya amfani da gasar wajen kai hari kan kasashen yamma.

Tawagar ta mutane 23, na kan hanyarta ne ta zuwa Afrika ta Kudu a ranar Lahadi, domin fafatawa a gasar da za a fara a watan Yuni.

Har ila yau sun gana da tsohon shugaban kasar Bill Clinton, da kuma mataimakin shugaban kasa Joe Biden.

"Wannan ba karamin abin alfahari bane, ganin yadda shugaba Obama da Bill Clinton da Joe Biden, suka tarbemu," a cewar shugaban hukumar kwallon kafa ta kasar Sunil Gulati.

Tawagar Amurka

Masu tsaron gida: Brad Guzan, Marcus Hahnemann, Tim Howard.

'Yan baya: Carlos Bocanegra, Jonathan Bornstein, Steve Cherundolo, Jay DeMerit, Clarence Goodson, Oguchi Onyewu, Jonathan Spector. 'Yan tsakiya: DaMarcus Beasley, Michael Bradley, Ricardo Clark, Clint Dempsey, Landon Donovan, Maurice Edu, Benny Feilhaber, Stuart Holden, Jose Francisco Torres. 'yan gaba: Jozy Altidore, Edson Buddle, Robbie Findley, Herculez Gomez.