Song na cikin jerin 'yan wasan 23 na Kamaru

Paul Le Guen
Image caption Cameroun Coach Paul Le Guen

Kocin Kamaru Paul Le Guen ya saka sunan tsohon dan wasan bayan Rigobert Song cikin jerin 'yan wasan 23 da zasu wakilci kasar a gasar cin kofin duniya.

Sunan Samuel Etoo na ciki duk da cewar Etoo din ya yi barzanar kauracewar gasar saboda sukar da Roger Milla yayi mashi.

Cikin jerin dai dan wasa daya ne tal ke buga kwallo a Kamaru wato Vincent Aboubakar wanda ke take leda Coton Sport striker.

Masu tsaron gida: Guy Roland N'Dy Assembe (Valenciennes), Idriss Carlos Kameni (Espanyol), Hamidou Souleymanou (Kayserispor)

Masu buga baya: Benoit Assou Ekotto (Tottenham Hotspur), Sebastien Bassong (Tottenham Hotspur), Gaetan Bong (Valenciennes), Aurelien Chedjou (Lille), Geremi (Ankaragucu), Nicolas Nkoulou (Monaco), Rigobert Song (Trabzonspor)

Masu buga tsakiya: Achille Emana (Real Betis), Enoh Eyong (Ajax Amsterdam), Jean Makoun (Olympique Lyon), Georges Mandjeck (Kaiserslautern), Joel Matip (Schalke 04), Landry Nguemo (Celtic), Alexandre Song (Arsenal)

Masu buga gaba: Vincent Aboubakar (Coton Sport), Eric Choupo-Mating (Nuremburg), Stephane Mbia (Marseille, France), Samuel Eto'o (Inter Milan), Mohamadou Idrissou (Freiburg), Achille Webo (Real Mallorca).