Eto'o ya yi barazanar kauracewa Kamaru

Eto'o
Image caption Eto'o na cikin tawagar Inter Milan data lashe kofina uku a bana

Dan wasan Kamaru Samuel Eto'o ya yi barazanar kin buga gasar cin kofin duniya a wata mai zuwa, bayan tsohon dan wasan kasar Roger Milla ya soke shi.

Eto'o ya shaidawa gidan talabijin na Faransa "shin ko akwai wata fa'ida ta zuwa na gasar cin kofin duniya?".

Ya kara da cewar"Ina da sauran kwanaki da zan kara tunanin ko zan taka leda ko kuma a'a".

Milla ya zama gwarzon dan kwallo ne bayan ya zira kwallaye hudu a lokacin da Kamaru ta kai wasan gabda na kusada karshe na gasar cin kofin duniya 1990.

A farkon wannan makon ne, Roger Milla yace Eto'o ya yiwa Barcelona da Inter Milan namijin aiki amma dai bai yiwa Kamaru komai ba.

Eto'o ya zira kwallaye 44 a wasanni 94 daya bugawa Indomitable Lions.

Kamaru na rukuni E tare da Netherlands da Denmark da Japan.