Prandelli zai zama kocin 'yan wasan Italiya

Prandelli
Image caption Kocin Fiorentina Cesare Prandelli wanda zai maye gurbin Lippi

Kocin Fiorentina Cesare Prandelli zai zama mai horadda 'yan wasan Italiya idan Marcello Lippi ya sauki bayan gasar cin kofin duniya.

Prandelli ana saran zai kulla yarjejeniya ta tsawon shekaru hudu kuma zai gabatar dashi a bainar jama'a bayan gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu.

Tsohon dan wasan Juventus din a baya ya taba zamowa kocin Parma da Roma .

Lippi me shekaru 61, ya taba lashe gasar serie A har sau biyar sannan kuma ya jagoranci Italiya ta lashe gasar cin kofin duniya a shekara ta 2006 kafin bayyana aniyarshi na sauka daga mukamin.