Ingila zata iya ba-zata -In ji Messi

Messi
Image caption Gwarzon dan kwallon duniya Lionel Messi

Dan wasan Argentina Lionel Messi ya ce Ingila na cikin wadanda zasu iya lashe gasar cin kofin duniya a Afrika ta Kudu.

Spaniya da Brazil sune kasashen da ake ganin zasu lashe gasar, amma dai dan wasan Barcelonan ya ce Ingila zata iya girgiza duniya.

Messi yace"Ina tunanin cewar a halin yanzu dai kasashen da suka fi karfi sune Spaniya da Ingila da kuma Brazil".

Kocin Ingila Fabio Capello ya riga ya bayyana cewar Argentina karkashin jagorancin Diego Maradona ita ce kasar dake bashi tsoro a gasar cin kofin duniya.