Real Madrid ta kaddamar da Mourinho a matsayin kocinta

Jose Mourinho

An gabatar da Jose Mourinho a matsayin sabon mai horas da 'yan wasan kulob din Real Madrid bayan ya sanya hannu a kan kwantiragin shekaru hudu da kulob din.

Mourinho dan shekara 47, ya maye gurbin Manuel Pallegrini ne don zama mai horas da 'yan wasan kulob din na goma sha daya a cikin shekaru bakwai da suka gabata.

"Ina son in kalubalanci kaina, wannan kuma babban kalubale ne da na baiwa kaina" in ji Mourinho.

"Ina da cikakkiyar yarda da kaina da kuma kokari na a matsayi na na mai horas da 'yan wasa.

Jose Mourinho ya koma kulob din na Real Madrid ne bayan tsohon kulob dinsa Inter Milan ya amince da kudaden fansa da Real Madrid suka biya.

Mai horas da 'yan wasan dan asalin kasar Portugal ya jagoranci kulob din Inter Milan wajen lashe kofin zakaru na nahiyar turai bayan sun lallasa kulob din Bayern Munich. hakan dai na nufin ya jagoranci kulob din wajen lashe kofuna uku a jere, wato kofin serie A da kuma kofin kasar Italiya.