Takaitaccen tarihin kwallon Chile

'Yan kwallon Chile
Image caption 'Yan kwallon Chile na fafatawa da Paraguay

Kasar Chile tun shekarar 1998 a kasar Faransa rabon data dandana romon gasar cin kofin duniya, kuma a wanan karon dai tana tinkaho ne tawagar data kunshi matasa wadanda zasu iya taka rawar gani a Afrika ta Kudun.

A lokacin wasannin share fage dai Chile ta kasance ta biyu daga yankin kudancin Amurka inda Brazil ta dara ta da maki guda.Wannan ne dai karo na takwas da Chile zata buga gasar cin kofin duniya kuma a shekarar 1962 ta samu kyautar tagulla matakin da bata kara kaiwa ba.

A bana dai Chile zata shiga gasar da karfinta ganin cewar 'yan wasanta kamarsu Matias Fernandez da Alexis Sanchez duk suna kan ganiyarsu.

Babban kalubalen dake gaban kocin kasar Marcelo Bielsa shine kokarin haskakawa a Afrika ta kudu kamar yadda ya haskaka a lokacin wasannin share fage inda suka samu galaba a wasanni goma.

Chile dai na rukunin H ne tare da kasashen Spaniya da Switzerland da kuma Honduras.