An dakatar da golan Masar Essam El Hadary

El Hadary
Image caption Golan Masar Essam El Hadary

Kotun hukunta laifukan wasanni CAS ta dakatar da golan Masar Essam El Hadary na tsawon watanni hudu.

Kotun ta kuma yanke hukuncin cewar dan wasan ya baiwa tsohuwar kungiyarshi wato Al Ahly diyyar pan dubu 750.

Yanke hukuncin ya kawo karshen takaddama tsakanin dan wasan da kungiyar Al Ahly akan komawar El Hadary kungiyar FC Scion ta kasar Switzerland.

El hadary dai ya fice daga Al Ahly ne a tsakiyar shekara ta 2008 inda ya koma Scion, abinda ya janyo Al Ahly ke cewar ya sabawa yarjejeniyar dake tsakaninsu.

El Hadary a yanzu yana bugawa Ismaili ne kuma dakatarwar tashi zata fara aiki ne a farkon kakar wasa mai zuwa.