Takaitaccen tarihin kwallon Ingila

'Yan kwallon Ingila
Image caption 'Yan kwallon kasar Ingila

Ingila dai bata fuskanci wata matsala akan hanyar ta na zuwa Afrika ta kudu ganin cewar ta samu nasara a wasanni tara na sharen fage inda Ukraine ce kadai ta samu galaba akanta.

Kuma gasar cin kofin duniya ta bana zata kasance wata dama ga zaratan 'yan wasan Ingila kamarsu Wayen rooney da Frank Lampard da kuma Steven Gerard don su nunawa duniya cewar abinda sukeyi a klub zasu iya yin mafinyin haka a kasarsu.

Wanann ne dai karo na 12 da ingila zata buga irin wannan gasar kuma sau daya ne tal wato a shekarar 1966 lokacin da ta dauki bakuncin gasar shine ta taba daga kofin. Kuma a shekarar 1990 ta kai wasan kusada karshe lokacin 'yan wasanta Gary Linker da Paul Gascoigne da David Platt inda Jamus ta fidda Ingila a wasan kusada karshe.

A halin yanzu dai babban kalubalen dake gaban kocin tawagar ingila wacce ake kira 'the three lions' wato Fabio Capello shine ya jagoranci kasar ta lashe gasar a Afrika ta kudu.

Ingila dai na rukunin C ne tare da kasashen Amurka da Algeriya da kuma Slovenia.