Arsenal ta ce ba za ta sayarda Fabregas ba

Fabregas
Image caption Kaptin din Arsenal Fabregas

Arsenal ta ki amincewa da bukatar Barcelona na sayen kaptin din ta Cesc Fabregas.

A ranar laraba ne Barcelona ta bayyana cewar ta gabatarwa Arsenal bukatar sayen dan wasan, wanda shima a baya yace yanason komawa Nou camp.

Sanarwar da Arsenal ta fitar, ta ce "mun samu bukatar Barcelona akan Cesc Fabregas a yammacin jiya, amma dai bamu da niyyar sayar da kaptin din mu".

Barcelona ta bayyana a fili cewar tanason Fabregas me shekaru 22 ya koma Nou Camp inda ya soma kwallo a matsayinshi na matashi.

Akwai rahotannin dake nuna cewar Barca na shirin bada pan miliyan 30 akan dan wasan duk da cewar watakila Arsenal ta bukaci nunkin kudin.