Shugaba Mills ya hana ministoci zuwa Afrika ta Kudu

Essien
Image caption Micheal Essien ba zai taka leda ba a Afrika ta Kudu saboda rauni

Shugaban Ghana John Attah Mills ya haramtawa ministoci da manyan jami'an gwamnati daga zuwa Afrika ta Kudu don su kalli gasar cin kofin duniya.

Shugaban ya ce wadanda keda aikin da suka shafi kwallo ne kadai zasu iya halartar gasar.

A cewar shugaban ma'aikatan fadar shugaban Ghana, John Martey Newman ya ce umurnin nada nufin tabbatar da cewa harkokin gwamnati basu fuskanci matsala ba lokacin gasar da za ayi a karon farko a nahiyar Afrika.

Tawagar Black stars na Ghana na cikin wadanda ake ganin zasu taka rawar gani daga cikin sauran wakilan Afrika kuma zata fafata ne da kasashen Jamus da Serbia da kuma Australia a rukunin D.

Ana saran shugaba Mills na daga cikin manyan bakin da zasu halarci wasan Black Stars na farko tsakaninta da Serbia a ranar 13 ga watan Yuni.